fbpx
Monday, August 8
Shadow

Wata Badurwa ‘yar shekara 16 ta kashe kanta ta hanyar rataya A Kano

Wani Al’mari mai cike da ban-mamaki  da  ya faru a yankin Zoo Road a cikin birnin jihar Kano, ya jefa mutane cikin mamaki da jamamin mutuwar wata yarin ya ‘yar kimanin shekaru 16 mai Suna Bahijja Gombe wacce ta kashe kanta ta hanyar rataya a ranar Asabar 14 ga watan Nuwamba.

Bahijja Gombe wanda rahotanni suka tabbatar da cewa, ta rataye kanta ne da misalin karfe 10 na dare A daki, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin mamaki da Al’hini.

Kamar yadda wata shadar gani da Ido, wacce ta bukaci a sakaya sunan ta, shada cewa, Bahijja ‘yar asalin jihar Gombe ce, Ana zargin ta kashe kanta ne ta hanyar rataya, sai dai, A cewar ta, Bahijja bata bar wata shaida ba na dalilin daukan wanna mataki.

Karanta wannan  Hukumar 'yan sanda ta damke wani matashi dayake yaudarar 'yan mata yana masu sata a jihar Legas

A ta bakin Jami’an rundunar ‘yan sanda DSP Haruna Abdullahi,  ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya shaida cewa tuni rundunar ta aike da gawar  Bahijja izuwa asibitin Murtala Muhammad dake jihar.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.