fbpx
Monday, June 27
Shadow

Wata dalibar UNILAG ta bata a jihar Legas tun ranar Alhamis, yan uwanta sun nemeta sama da kasa basu ganta ba

Wata matashiya yar shekara 20, Arafat dalubar jami’ar UNILAG ta jihar Legas ta bata inda ‘yan uwanta suka bayyana cewa sun nemeta sama.da kasa amma basu ganta ba.

Manema labarai na Tribune sun ruwaito cewa Arafat ta bar gida ne a ranar alhamis 26 ga watan mayu.

Inda mai rainon Arafat din ya bayyana cewa ta bar gida ne da misalin karfe biyar na safe ranar alhamis kuma har yanzu basu ganta ba.

Yace sun nemeta sosai har a makaranta kuma sun sanar da hukumar ‘yan sanda, inda suka ce masu an sanar a sauran ofisoshin da kuma gidajen rediyo.

Leave a Reply

Your email address will not be published.