fbpx
Monday, March 1
Shadow

Wata kila mu rushe Gadar kofar Nasarawa mu sake wata>>Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce akwai yiwuwar zata rushe Gadar Sama ta Kofar Nassarawa da ke cikin birnin Kano tare da Gina wata sabuwa.

 

Kwamishinan yada labarai na jihar, Mallam Muhammadu Garba ne ya bayyana hakan, a yayin daya karbi bakuncin wata Kungiya mai goyon bayan Gwamna Ganduje a Ofishin sa.

 

Kwamishi nan ya ce a halin yanzu gwamnatin Kano tana yin nazari akan yadda gwamnatin baya ta aiwatar da ginin Gadar.

 

Ya kara da cewa mai yiwuwa idan gwamnatin ta kammala nazari da bincike to zata ruguje Gadar tare da gina sabuwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *