fbpx
Tuesday, January 19
Shadow

Wata kotu ta tsare wata Yar aikin gida mai shekaru 23 a kan yin kurin sace maigidanta

Wata Kotun Majistare da ke Osogbo ta tura wata ’yar aikin gida mai shekaru 23, Olayemi Lawrence kan zargin sata da yunkurin sace maigidan nata.

 

An tuhumi matar da ake zargi da laifuka guda biyar da suka hada da hadin baki, sata, yunkurin kona gida da kuma yunkurin sace maigidan nata.
Wadda ake zargin ta aikata laifin ne a watan Disamba na shekarar 2020 da misalin karfe 2 na dare a Ilasa-Ijesha da ke Obokun.
Mai gabatar da kara na ‘yan sanda, ASP Abiodun Fagboyinbo ya fadawa kotun cewa wanda ake zargin ta fasa gidan wata mata mai suna Misis Eunice Abike Fateye da ke gida mai lamba 5 Orofon kuma ta saci wayar Itel P36 da kuma wata wayar hannu ta android da kudinta ya kai N150,000.
“Ta saci katin ATM na UBA kuma ta yi amfani da shi wajen cire kudi N305,000 daga asusun ta na UBA mai lamba 20533055990 sannan kuma ta yi barazanar sanyawa gidanta wuta idan ta ki tura kudin N500,000.”
Mai gabatar da karar ya kuma yi zargin cewa wanda ake zargin ta yi yunkurin yin awon gaba da maigidan nata ta hanyar tura mata sakonnin tes a rubuce idan har ta kasa turo mata kudi N500,000.
Wadda ake tuhumar ta musanta laifin da ake tuhumar ta da ita.
Lauyan da ke kare wanda ake kara, Mista Nagite Okobe, ya roki kotun da ta ba wa wadda yake kare belin a kan mafi yawan lokuta na sassauci tare da tabbatar da cewa tana da amintattun mutane da za su tsaya mata a shari’ar.
Mai gabatar da kara, Fagboyingbo ya ki yarda da belin. Yana mai cewa za ta yi guduwa idan aka bayar da ita kuma ran wadda ta shigar da karar zai kasance cikin hadari saboda wakilan wanda ake zargin sun yi barazanar rayuwar Cif Faleye.
Alkalin Kotun, Mista Adebayo Ajala ya mika batun zuwa Kotun Majistare ta Ibokun a kan cewa laifin da ake zargin an aikata a wannan yankin.
Ya ba da umarnin a tsare ta a Cibiyar Kula da Gyaran hali ta Ilesa.
An daga karar zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2021 don sake gurfanar da ita.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *