fbpx
Monday, March 1
Shadow

Wata mata da jaririnta sun jikkata sakamakon fashewar iskar gas a Jihar Kano

Wata matar gida da jaririnta sun jikkata bayan fashewar iskar gas a jihar Kano.

Fashewar iskar gas din ya faru ne da sanyin safiyar Litinin, 15 ga Fabrairu, wanda ya kai ga lalata gini da wasu kadarori.

Fashewar ta afku ne sakamakon fashewar iskar gas din girkin na gida.

An bayyana cewa an dauki matar da yaron da suka jikkata a cikin motar daukar marasa lafiya zuwa International Clinic amma an tura su Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, inda yanzu haka suke karbar magani.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *