Wata mata me sunan Imole a yankin Idimu na jihar Legas ta zubawa ‘yar uwarta Fetur ta kunna mata wuta tare da ‘ya’yanta 3.
Lamarin ya farune saboda rigimar Rabon gado da ya barke a tsakaninsu. Inda ita Imole ta je wajan ‘yar uwartata ta nemi a bata kasonta na dakuna 4 da mahaifinsu ya bari.
Saidai ‘yar uwarta ta bayyana mata cewa daki 1 kawai zata samu saboda akwai sauran ‘ya’yan mahaifinsu da suma suna da Kaso a ciki. Wannan abu bai yiwa Imole dadi ba inda su kai ta cece-kuce amma daga baya ta tafi.
Hutudole ya fahimci an zargi Imole da dawowa cikin dare ta fasa taga ta zuba fetur a cikin gidan da ‘yar uwartata take da ‘ya’yanta 3 da kuma mijinta ta banka musu wuta suka kone. An garzaya dasu Asibiti inda ita kuma ta tsere.
Wami shaida, Femi, ya bayyanawa Vanguard cewa matar data yi wannan aika-aika ana zargin tana da tabin hankali. Yansandan yankin sun tabbatar da faruwar lamarin inda suka ce ana kokarin kama Imole sannan kuma za’a mata gwajin lafiyar kwakwalwa.