fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Wata mata ta kashe mijinta da wuka kan ya kamata tana lalata da mace ‘yar uwarta a jihar Anambra

Wata mata ta kashe mijinta Ikechukwu kan ya kamata tana yin lalata da mace ‘yar uwarta a Onitsha jihar Anambra.

Ikechukwu ya kasance ma’aikaci a kwalejin kiwon lafiya dake Onitsha a jihar ta Anambra, kuma ya kama matar tasa tana yin lalatar ne bayan ya dawo gida a ranar talata.

Inda suka fara cacar baki domin abin ya bata masa rai saboda bai taba sanin cewa matar tasa ‘yar madigo bace sai a ranar, inda kuma ta caka masa wuka ya mutu.

Amma hukumar ‘yan sanda ta kamata tare da kawar tata kuma wannan lamarin ya matukar tayar da hankulan al’ummar yankin domin mijin nata ya samu shaida mai kyau a wurin jama’ar.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.