Wata ‘yarsanda me suna Ruth ta kama hannun diyar ‘yar uwarta ta tsoma a cikin ruwan zafi saboda satar nama.
Ruth na zaunene a Dutsen Alhaji dake babban birnin tarayya, Abuja. Kuma abinda ta aikata ya farune a lokacin kirsimeti.
Ta kama yarinyar me suna Miracle na daukar nama daga tukunyar da take dafa abinci.
Wani shaida ya bayyana cewa yaga yanda Ruth ta daure hannayen Miracle 2 ta tsomasu a tafasashshen ruwan zafi.
An garzaya da yarinyar Asibiti, kakakin ‘yansandan Abuja, DSP Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin.