fbpx
Saturday, September 23
Shadow

Wata mata ta mutu bayan data samu labarin mijinta ya kamu da cutar coronavirus

Lamarin dai ya faru ne jihar Delta a ranar litinin.

Matar waccea ke zaune a  Igho dake kan titin Salami Uloho Avenue Ughelli, rahotanni sun bayyana cewa matar ta yanke jiki ta fadi a lokacin da aka zo mata da labarin cewa mijin ta ya kamu da cutar Coronavirus.

Lamarin da ya jefa mazaunan yankin da makotan matar cikin al’hini da jimamin faruwar al’amarin.

Yadda abin ya faru shine matar mai suna Oregbe an rawaito cewa a lokacin tana zaune a gida a ranar litinin sai sakamakon gwajin da a kaiwa mijin ta, na cutar Korona ya fito inda sakamakon ya tabbatar da mijin nata ya kamu da cutar, nan take matar da ake kira da Oregbe ta yanke jiki ta fadi kamar yadda shaidu suka tabbatar.

Matar dai ta mutu ne a sakamakon jininta da hau matuka wanda hakan yayi sanadin ajalinta.

Sai dai a lokacin da aka tuntubi hukumar ‘yan sandan jihar sun tabbatar da cewa lalle basu da masaniya akan hakan domin ba a sanar da su rahoton hakan ba. Kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *