fbpx
Monday, December 5
Shadow

Wata mata ta zargi wani sanatan kasar Amurka da taba mata jiki ba tareda izininta ba: Ya nemi afuwa: kuma ya bukaci a bincikeshi

Wannan hoton wani sanatan kasar Amerikane me suna Alfranken da wata tsohuwar abokiyar aikinshi me suna Tweeden ta zargeshi da taba mata jiki ba tare da izininta ba. lokacin yana dan wasan barkwanci a shekarar 2006. Lamarin ya farune lokacin da abokan aikin biyu tare da wasu ma’aikata suka tafi gabas ta tsakiya gurin sojojin kasar ta Amurka dan nishadantar dasu.

Bayan sun isa kasar ne sai aka sanar da Tweeden cewa itama tana cikin wadanda zasu yi wasan na barkwancin kuma ana bukatar ayi sumbata a cikin wasan, a ranar da zasu gabatar da wasanne sai Alfranken ya bukaci suyi gwajin yin sumbatar shida Tweeden amma taki yarda, bayan ta saki jikine sai Franken ta lallabo ya kamo ta ya sumbaceta da karfi har sai da ta tureshi kuma ta gargadi kada ya kara mata haka.

Alfranken ya amsa laifinsa inda yace duk da cewa bazai iya tuna ainihin abinda ya faru ba a wancan lokacin amma yana neman afuwar matar dama duk wadanda sukayi aiki dasu tare a wancan lokacin da kuma sauran al’umma, ya kuma kara da cewa shi mutum ne me son kare hakkin mata duk da cewa abinda ya aikata zai sa mutane suyi kokwantonshi amma baya shiri da wanda bai son kare hakkin mata kuma yaji kunyar abin da ya faru sosai.

Karanta wannan  Saboda Tsantsar Son Musulunci Mahaifiyar Tinubu Ta Gagara Zama A Landan A Lokacin Da Ake Jinyar Ta A Can Saboda Ba Ta Jin Kiran Sallah, Cewar Kabiru Gombe

Haka kuma Tweeden ta sake ballowa Alfarnken wani sabon abin kunyar inda ta bayyana wannan hoton da ake gani a sama tace bayan da ya sumbace ta da karfin, ba tare da son rantaba sai tayi kokarin ganin ta dena zama kusa dashi ko kuma kebewa tare dashi har suka koma kasarsu ta Amurka.

Amma wani abin mamaki sai taga wancan hoton na sama yana yawo a tsakanin mutane Alfranken din ya na nuna shi inda ya taba jikinta lokacin tana bacci.

Shima dai akan wannan abin Alfranken ya nemi afuwa inda shi da kanshi ya nemi ayi bincike akan halayyarshi kuma a dauki matakin da ya dace na shari’a.

A lokacin yakin neman zaben shugaban kasar Amurka Donald Trump shima an zargeshi da yin kalaman batsa .


Faifan bidiyon tsohon gwamnan jihar Yobe Bukar Abba Ibrahim yana lalata da wasu mata 


Bukar Abba Ibrahim ya mayar da martani akan hoton biyon da ya watsu inda aka ganshi yana lalata da wasu mata

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *