Wasu alamu sun nuna cewa ga dukkan mai yiyuwa kwaikwakayar sa hannun babban alkalin kotun tarayya dake Kano aka yi aka fitar da hukuncin kotu na karya da yace a cire sarki Muhammad Sanusi II daga kan kujerar sarautar Kano.
A wani bincike da Kafar Daily Nigerian ta yi, ta gano cewa sa hannun da aka gani a takardar data dakatar da sarkin ta banbanta da sauran sahannun da alkalin ya saba yi.
Kuma a baya, Alkalin yakan saka hannu a duka takardun hukunci ne amma a na hukuncin da ya sauke sarkin, a takardar karshe ce kawai aka saka hannun.
Hakanan kuma Akwai wanda ake tuhuma a takardar kotun su 8 amma cikinsu babu wanda baiwa kwafin takardar sai kwamishinan ‘yansandan jihar kadai.
Wannan yasa ake zargin cewa takardar ta boge ce.