fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Wata Sabuwa da duminta:Gwamnatin tarayya ta fara binciken Atiku dan kwato wasu makudan kudade da ake zargin ya sata

Gwamnatin tarayya ta hada kai da wani kamfanin kasar Amurka dan kwato wasu makudan kudade da ake zargin dan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sata.

 

Sauran wanda ake zargi tare da Atiku sune tsohon gwamnan jihar Ekitix Ayodele Fayose da kuma Sanata Musuliu Obanikoro, kamar yanda jaridar The Cable ta ruwaito.

 

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a,  Abubakar Malami ne ya bayyana haka a wasikar da ya aikewa kamfanin.

 

Ya roki kamfanin da ya taimakawa Najariya a kwato wadancan kudaden.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.