Shararren mai kudin kasar Amurka dake shirin sayen Twitter, Elon Musk yayi barazar fasa sayen kafar sada zumtar.
Elon Musk na shirin sayen Twitter ne a farashin dala bilyan 44, amma yanzu yana shrin fasawa saboda akwai lauje cikin nadi tsakin shi da masu kafar sada zumuntar.
Inda lauyansa ya bayyana cewa masu kafar sada zumuntar sunki baiwa Musk damar duba Twitter yadda ya kamata domin akwai asusun bogi da yawa a cikinta.