Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya bayyana cewa, an mikawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari bincike na farko da aka yi akan harin da Boko Haram suka kai gidan yarin Kuje dake babban birnin tarayya, Abuja.
Yace idan aka ji wadanda ke da hannu a lamarin, hankula zasu tashi.
Yace kuma akwai jami’an hukumar tsaron gidan yarin da ake zargi da sakaci wajan rashin daukar marakan da suka dace sannan kuma akwai wadanda ake zargi da bada hadin kai wajan yin harin.
Yace duk wanda aka samu da hannu za’a hukuntashi.
Ya bayyana hakane bayan zaman majalisar tsaro ta kasa da ya wakana a yau, Alhamis a Abuja.