fbpx
Thursday, March 4
Shadow

Wata Sabuwa: Kotu ta yankewa wani dalibi hukuncin daurin watanni 6 a gidan yari saboda satar karnuka

Wata Kotun majistare a Jihar Jos ta yanke wa wani dalibi mai shekaru 15 hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni shida saboda satar karnuka biyu.

Wani kwamitin alkalai biyu, Ghazali Adam da Hyacinth Dolnaan, wadanda suka yanke wa Ibrahim hukunci bayan ya amsa laifin, amma, sun ba shi zabin ya biya tarar N20,000 ko kuma ya shafe watanni uku a kurkuku.

Mahukuntan sun kuma umarci mai laifin da ya biya N50,000 a matsayin diyya tare da daurin watanni uku a gidan yari.

Alkalan sun ce wannan hukuncin zai zama darasi ga wadanda suke son aikata irin wannan laifin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *