fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Wata Sabuwa: Kwayar Cutar Yunwa Tafi Illata Yan Najeriya Sama da Coronavirus A cewar Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar II yayi Kira da gwamnati da ta dauki matakan gaggawa don inganta rayuwar ‘yan Najeriya, yana mai cewa “cutar yunwa” tana kashe’ yan Najeriya fiye da tsoron cutar COVID-19 (Coronavirus).

 

Mai alfarma Sarkin wanda ya yi jawabi a taron farko na Majalisar Addinai ta Najeriya (NIREC), a Abuja, ranar Alhamis, inda yace ko da yake, Cutar Coronavirus na kashe daruruwan mutane a fadin duniya, ”

 

Amma a cewarsa cutar yunwa” ita ce babbar cutar da take kashe ‘yan Najeriya.

 

Ya kuma Kara da cewa shin akwai kwayar cutar da ke kashe ‘yan Najeriya da ta fi Coronavirus girma. Inda ya bayar da amsa da cewa wannan kwayar cutar itace yunwa.

 

A cewarsa kwayar cutar yunwa tana da matukar tsanani. Inda ya bayyana da cewa ya kamata ku zagaya cikin ƙauyuka, cikin birane don ganin yadda mutane suke ƙoƙari sosai don tsira.

 

Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, a cikin jawabinsa a wajen taron, ya sake baiwa shugabannin addinai tabbacin cewa, gwamnatin kasar ta yi matukar himma don ganin an samu ci gaba da zai magance talauci ga ‘yan Najeriya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.