fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Wata Sabuwa: Sadakar marigayi sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero na neman dauki: “Iyalanshi sunyi watsi da ita da ‘yayanta bayan rasuwarshi”

Wata mata me suna Hauwa Momoh wadda tayi ikirarin cewa ita sa dakar tsohon sarkin Kanoce, Marigayi Alhaji Ado Bayero, ta koka akan yanda bayan rasuwarshi iyalinshi sukayi watsi da ita da ‘ya’yanta guda biyu suka shiga halin kakanikayi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Hauwa wadda kafar watsa labari ta jaridar Punch ta zanta da ita lokacin bata da lafiya a garin Legas, ta nunawa wakilin jaridar maganin da wani bawan Allah me tausayi ya siyamata, domin bata da me taimako sai Allah, ta bayyana cewa rayuwarta tana cikin hadari.
Da farko dai ta bayyana cewa iyalan marigayin sarkin sun gargadeta da cewa kada ta sake tayi magana da wata kafar watsa labari akan halin da take ciki, idan kuwa ta kiya, zata gayawa ‘yan garinsu.
Mahaifin Hauwa wanda tsohon basaraken garin Auchi ne na jihar Edo, marigayi Ahmed Momoh, abokaine na kut da kuta da tsohon sarkin Kanon, kuma a shekarar 1984 ya damka Hauwa a hannun sarkin Kanon ne dan ya zama me kula da ita da kumawa wajan samamata damar shiga jami’ar Ado Bayero dake Kanon.
Amma daga karshe sai labari ya canja, soyayya ta shiga tsakanin sarkin Kanon da Hauwa, har a shekarar 1986, ta samu ciki, ta haihu.
Hauwa tace duk da cewa sarkin be auretaba, amma sai mahaifinta ya amince da soyayyar da takeyi da sarkin, kuma shekaru shabiyar bayannan ta sake haihuwa dashi.
Tace sarkin ya gina mata gida a unguwar gandun Albasa inda suka ci gaba da ganawa tare na tsawon shekarau talatin da biyu, har zuwa lokacin da ya rasu a shekarar 2014.
Tace duk da yake iyalan na sarkin sun amince da ‘ya’yan da ta haifa dashi amma suna nuna musu wariya, ta kara dacewa sarkin mutumoin kirkine kuma lokacin yana raye, ya kula dasu sosai, basu taba shiga cikin wata matsala ta azo a ganiba, amma yana rasuwa, daya daga cikin ‘ya’yanshi ya dauki alkawarin kula da ita da ‘ya’yanta amma, sai iyalan nashi, daga baya, suka koreta ita da ‘ya’yanta daga cikin gidan da sarkin ya gina mata, akama rushe gidan, yanzu haka ta bayyana cewa ‘ya’yan nata ko makaranta baa zuwa.
Tace haka take ta tangaririya akan titi bata da gurin zama, ta bayyana cewa akwai loacin da wata kafar watsa labarai ta yanar gizo taso tayi hira da ita, da iyalan marigayin sukaji, sun aiko wau ‘yan sanda, lokacin tana Abuja, suka gargadeta, da kada ta sake tayi wani shirme, in ba haka ba, Tam!.
Ta kara da cewa, jami’an tsaron ‘yan sanda dake kula da kare harkar fashi da makami da da kwanannan aketa kiran a sokesu, watau, SARS, sun shiga nemanta ruwa a jallo, tace wani lokacin da suka zo nemanta, sai wani bawan Allahne ya boyeta, basu ganta ba suka wuce.
Tayi kira ga mahukunta, musamman a garin Legas da su taimaka mata, haka kuma tace sarkin a wasiyyar da ya bari ya bukaci a kula da ita da ‘ya’yanta amma iyalan nashi basa kare martabar marigayin mahaifin nasu, injita, kuma ta bayyana cewa ana mata irin wannan cin kashinne kawai saboda ba daga yankin Arewa ta fitoba.
Da jaridar tayi kokarin jin ta bakin ‘ya’yan na marigayi, Ado Bayero, ta tuntunbi Aminu Ado Bayero wanda ya bayyana cewa bashi da hurumin yin magana akan wannan batu, inda ya nunasu zuwa ga dan uwanshi Sanusi Ado Bayero.
Shi kuwa Sanusi ya bayyana cewa a musulunce ba alhakin iyalan marigayin bane su kula da Hauwa da ‘ya’yantaba, kuma ya karyata ikirarin da Hauwa tayi na cewa wai basu mata komai ba, yace a tambayeta atji, sun taimaketa, sun mata komai, kusan duk suna taimakonta, amma bata da godiyar Allah ga kuma kashe kudin tsiya.
Jaridar ta Punch tayi kokarin jin ta bakin hukumar ‘yan sanda dake kula da fashi da kami ta SARS inda taso taji ta bakinsu akan akan zargin da Hauwa tayi cewa jami’anta suna nemta ruwa a jallo, amma wayar da jaridar ta buga ba’a dagaba.
Allah shi kyauta.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele, kuma DSS sun kamashi

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *