fbpx
Monday, May 23
Shadow

WATA SABUWA: Shi Ma Dan Kwallon Nijeriya, Ahmed Musa Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa A Zaben 2023

WATA SABUWA: Shi Ma Dan Kwallon Nijeriya, Ahmed Musa Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa A Zaben 2023.

Shahararren dan wasan kwallon kafa ta Super Eagles ta Nigeria, Ahmad Musa, zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a kasar nan a zaben 2023.

Shehu Abdullahi, abokin wasansa ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a yau Talata, 10 ga watan Mayu.

“Ahmad Musa zai bayyana tsayawa takarar shugaban kasa a sati mai zuwa” in ji Shehu Abdullah

Wannan na zuwa ne bayan da mutane da dama suke ci gaba da bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban cin kasar nan musamman a jam’iyya mai mulki ta APC wadda kawo yanzu aka tabbatar da Kusan yan takara 30 ne suka nuna sha’awarsu ta tsayawa takara.

Karanta wannan  Hotuna:'Yar shekaru 84 ta sayi fom din takarar majalisa a Borno

Ahmad Musa dai ya buga kwallo a kungiyar Kano, Pillars da VVV Venlo ta kasar Netherlands sai CSKA Moscow ta Russia sannan ya buga wasa a Leceister City ta Ingila sai Kuma kungiyar Al-Hilal ta kasar Saudiyya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.