Shugaba Muhammadu Bubari ya rantsar da Olukayode Ariwoola a matsayin shugaban alakalan Najeriya na wucin gadi bayan Ibrahim Muhammad Tanko yayi murabus ranar litinin.
Amma fa akwai lauje cikin nadi domin takaddun makarantarsa na nuna cewa an hafesa ne a ranar 22 ga watan Augusta na shekarar 1958,
Kuma ya fara makarantar firamari a shekarar 1959 wanda hakan ke nuna cewa ko shekara guda bai kai ba yayin daya fara zuwa makaranta.
Lauyoyin arewacin Najeriya sun kalubalanci rantsar da Ariwoola matsayin shugaban lauyoyin Najeriya,
Inda suka ce shima ba wata isasshiyar lafiya ce dashi ba saboda haka ba zai iya aiki yadda ya kamata ba, kuma shima Tanko wannan dalilin ne ya saka shi yayi murabus.