Wani Sabon bincike da aka yi ya nuna cewa sai nan da shekarar 2028 sanna za’a samu damar yiwa kaso 75 na mutanen Duniya rigakafin cutar Coronavirus/COVID-19.
Binciken na alamta cewa sai an kai wancan lokacine sannan Duniya zata samu Nutsuwar cewa an fara bankwana da Annobar cutar Coronavirus/COVID-19.
Kafar yada labatai ta Bloomberg ta bayyana cewa, amma kasar Amurka, nan da zuwa farkon shekarar 2022 ne zata samu kaiwa wannan matsayi.
Zuwa yanzu dau kasar tawa kaso 8.7 na mutanen ta rigakafin cutar.