fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Wata sabuwar annoba ta sake barkewa a kasar Chana

Bayan cutar sarkewar Numfashi ta Covid-19, wata sabuwar annoba ta sake barkewa a kasar Chana.

Sunan wannan sabuwar annobar Langya kuma ta kama mutane da dama a kasar kusan 36 na dauke da cuar amma har yanzu bata kashe kowa a cikinsu ba.

Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa daga dabbobi ake samun cutar ta Langya kuma tun a shekarar 2018 ta bullo amma sai makon daya gabata hukumar kiwon lafiya ta Taiwan ta gano annobar.

Kuma cutar na sanya ciwon jiki da zazzabi da tari da dai sauran su, yayin da hukumar kiwomn lafiyar ke cigaba da bincike akan cutar domin a magance ta.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.