Shugaban hukumar kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC, Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa wata sabuwar nau’in cutar Coronavirus/COVID-19 ta shigo Najeriya.
Yace wannan sabuwar nau’in na cutar sunansa B1.2.5 sannan yana da banbanci da B1.1.7 da ta shigo a kwanakin baya.
Yace yanzu cutar ta shiga kasashen Duniya 15 kenan. Ya bayyana hakane ranar 22 ga watan Fabrairu yayin ganawa da manema labarai.
Yace amma wannan sabon nau’in cutar ba’a tantance ko yana da wana illa ta musamman ba ko kuwa a’a.