fbpx
Saturday, March 25
Shadow

Wata sananniyar me gabatarda shirye-shirye, Rachel ta ziyarci IBB: Sunsha hannu har sau biyu: Ta yabeshi sosai

Wata sananniya me gabatar da shirye-shirye a kafafen watsa labari kuma ‘yar rasjin kare hakkin bil’adama me suna Rachel Bakam ta kaiwa tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida(IBB) ziyara a gidanshi dake kan dutse a jihar Naija.

Rachel ta wallafa wadannan hotunan a dandalinta da sada zumunta da muhawara inda ta bayya irin yanda tsohon shugaban yake birgeta saboda irin karamcinshi da kyawawan haleyenshi, da basira, da nutsuwa dake tattare dashi da kuma yanda yake sauraron mutane idan suna magana dashi, injita.

Haka dai wannan baiwar Allah tayi ta zuga tsohon shugaban kasar, kuma tace ita da tawagarta sun mikawa IBB din wani katin godiya da gaisuwa haka kuma ta kara da cewa abinda ya kara birgeta shine irin yanda ya dauki lokaci ya karanta katin da suka kai mishi.
Haka kuma Rachel din ta yabi tsohuwar matar IBB din marigayiya Maryam Babangida inda har ta tuna da shaharren daurin dan kwalinnan nata da ya amsu tsakanin matan Najeriya a wancan lokacin sannan kuma ta mata addu’a.
Bayan da suka sha hannu har sau biyu  kuma Rachel din ta mikawa IBB din katin da ta kaimishi, sai ta zagaya cikin gidan nashi inda ta dauki hotuna.
 Anya kuwa tsohuwar jarumar fina-finan Hausa Ummi Zeezee bazata yi kishi ba idan taga yanda wannan matar ta ziyarci IBB da kuma yanda take yabonshi?

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Ya Rasu Bayan Kammala Alwallar Sallar Magariba Ta jiya Juma'a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *