fbpx
Friday, August 12
Shadow

Wata mata ta koka bayan yaron mai gidansu ya lakadawa mahaifuyarta duka har ta mutu a jihar Anambra

Wata mata a jihar Anambra, Mmesoma Ekpe ta koka bayan yaron mai gidan da suke haya a ciki ya kashe mata mahaifiyarta ranar asabar.

Mmesoma ta bayyana hakanne a wani bideyo inda tace yaron mai gidan, Ebube Oba ya lallasa mahaifiyarta Uzomaka Ekpe har ta mutu.

Inda tace rikicin ya fara ne yayin da yaron ya cewa gabadaya mutanen gidan dake Onisha su tsafatace shi tas duk da cewa suna biya ana tsaftace gidan a kowane wata.

Kuma ya hana gabadayan mutanen gidan fita wurin ayyukansu inda har ya hanata fita wanda hakan yasa suka fara cacar baki da mahaifiyarta har ta kaiga ya fara dukanta, kuma ya nausheta a girji ta mutu.

Karanta wannan  Yaro dan shekara 12 ya kashe mahaifiyarsa da bindiga 'yar Najeriya a kasar Amurka

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.