Wata yarinya Sa’adiya Umar ‘yar shekara 16 ta kashe kanta ta hanyar rataya sakamakon auren dole da iyayenta suka yi mata.
Wannan lamarin ya faru ne a kauyen Garin Dauru dake karamar hukumar Warawa a jihar Kano.
Kuma mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda na jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin.
Inda yace a ranar daya ga watan Augusta ne mai garin ya sanar dasu kuma an kaita asibiti inda wa’adinta ya cika a can.