fbpx
Thursday, July 2
Shadow

Watakila Jadon Sancho yayi irin yarjejeniyar Cristiano Ronaldo wadda zata sa shi ya koma Manchester United

Borussia Dortmund sun yarda cewa Sancho zai bar kungiyar su a wannan kakar wasan saboda Manchester United sun nemi shi a shekarar data gabata, a cewar gwanin Bundlesliga kuma tsohon dan wasan Norway Jan Age Fjortoft.

Jadon Sancho shine babban dan wasan da Man United zasu siya idan aka bude kasuwar yan wasa, yayin da dan wasan Ingilan yayi nasarar jefa kwallaye guda 17 kuma ya taimaka wurin cin kwallaye guda 16 a wannan kakar wasan. Fjortoft ya tabbatar da cewa Dortmund sun san Sancho yana so ya bar su a wannan shekarar.
Mai sharhin wasannin ya gayawa ESPN FC cewa, a koda yaushe Dortmund suna fatan adana yan wasan su amma daga karshe kuma su rasa su. Shi yana jin cewa a kakar wasan bara Dortmund sunyi irin yarjejeniyar da Ronaldo yayi da United yayin da Sir Alex Ferguson yace mai ba zai bar shi ya koma Real ba a halin yanzu, ya tsaya ya kara buga wani kakar wasa kuma yayi iya bakin kokarin shi sannan su bar shi ya tafi.
Ya Kara da cewa Sancho yaci kwallaye uku a wasa daya (Hat trick) yana kokari sosai, yana taimakawa wurincin kwallaye, shekarun shi 20 kacal kuma shi dan Ingila ne saboda haka akwai kungiyoyin Ingila da dama da zasu iya biyan makudan kudade wajen siya  shi, kuma zai to matukar mamaki idan Sancho bai bar Dortmund yanzu ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *