Sabbin jami’an hukumar NDLEA da aka dauka sun koka da cewa watanni 7 da aka dauke su aiki ba’a biyasu Alawus ko Albashi ba.
Ma’aikatan sun ce an musu alkawarin za’a biyasu hakkokinsu a watan Fabrairu amma hakan bata samu ba.
Daya daga cikin ma’aikatan ya shaidawa majiyarmu cewa shi abin ya isheshi ace mutum ya fara aiki amma ba Albashi.
Ma’aikatan da basuso a bayyana sunayensu ba, sun bayyana cewa, suna rokon a taima a biyasu hakkokinsu.