fbpx
Monday, August 8
Shadow

West Ham 1-3 Manchester United: Yayin da Manchester United tayi nasara karo na tara a jere a wasannin daba na gida ba tare da cin kwalllaye biyu a wasannin

Manchester United ta zamo kungiya ta biyu a gasar Premier league data yi nasara a wasanni tara a jere wanda bana gida ba kuma tare da cin kwallaye biyu a wasannin, tun bayan da Leeds tayi hakan a watan afrilu na shekara ta 2001.

United tayi nasasar lallasa West Ham ne ta hannun Pogba,Greenwood da kuma Rashford. Kwallon Greenwood ta kasance ta 20 daya ci tun farkon kakar data gabata, kuma hakan yasa ya zamo dan wasa mafi karancin shekaru daya ci kwallaye masu yawa yayin da kwallayen nashi suka ninka na Martinelli wanda yaci 10.

Karanta wannan  Bideyo: Ronaldo baiji dadin ajiye shi a benci ba da Yen Hag yayi

Tauraron dan wasan United na tsakiya, Bruno Fernandez yayi nasarar taimakawa kungiyar da kwallaye 36 a wasanni 38 daya buga tunda ya koma kungiyar a watan febrairu, bayan daya ci 22 kuma ya taimaka wurin cin 14 wanda hakan yasa ya fi gabadaya yan wasan Premier league da kwallaye biyar a wannan lokacin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.