A jiyane gwamnan jihar Ekiti Ayodele fayose yayi murnar zagayowar ranar haihuwarshi, a cikin maganganun da yayi yace yayi fatan ace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tayashi murnar zagayowar ranar haihuwar tashi, wani bawan Allah da yake bibiyar lamurran gwamnan yace yana fatan kada Allah ya yayi watsi da lamuran mu kamar yanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi watsi da gwamnan duk da kokarin babatun da yake yi na ganin ya tsokani sugban.
Matashin dai yayi rubutu a dandalinshi na sada zumunta da muhawara na shafin Twitter akan gwamnan, da ya dauki hankulan mutane da yawa kamar haka:
Lallai Shugaba Buhari ya cika mutum me dattako, Gwamna Fayose ya shafe shekaru biyu da rabi yana ta tsokanarshi amma baba( Buhari yayi watsi dashi kamar bai san Allah yayi ruwan tsirarshiba. Ina fata kada Allah yayi watsi da lamurranmu kamar yanda shugaba Buhari yayi watsi da gwamna Fayose.