Wani jigo a kungiyar kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ya bayyana cewa ya kamata a duba irin abubuwan da kungiyar IPOB ke yi a basu shugabancin Najeriya.
Chuks Ibegbu ya bayyana cewa ba gaskiya bane abinda IPOB keyi wai yasa yanzu ba za’a yadda dasu a basu shugabancin Najeriya ba.
Yace maimakon haka ma kamata yayi ace abinda IPOB dun ke yi ma yasa ‘yan Najeriya zu gaggauta baiwa Inyamurai shugabancin Najeriya.
Yace kowane yanki a Najeriya sun samar da shugaban kasa duk da matsalolin tsaron dake faruwa a yankunan dan haka suma abinda IPOB ke yi bai kamata yasa a hanasu shugabancin Najeriya ba.