fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Ya kamata a yiwa Dazukan Najeriya rugu-rugu da ruwan bamabamai daga baya an sake shuka wasu itacen>>Gwamna El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayar da shawarar cewa domin magance matsalar tsaro, shi yana ganin a yi rugu-rugu da dazukan Najeriya da ruwan bamabamai daga baya an sake shuka wasu itacen.

 

Gwamnan ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Arise TV inda yace rashin isassun kayan aiki ga sojoji ne ya kawo wannnan matsalar.

 

Yace idan da za’a samarwa sojoji da isassun kayan aiki to da lallai an kawo karshen matsalar tsarom da ake fama da ita.

Karanta wannan  Labari me dadi: An kwato buhunan takin zamani da 'yan ta'adda suka siya dan hada bamabamai

 

Gwamnan ya kara da cewa, babu jihar da bata fama da nata matsalar tsaron yace kuma babban abinda ke kawo tsaiko ga maganace matsalar shine rashin isassun kayan aiki.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.