fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Ya kamata ASUU ta karbi wannan tayi na Gwamnatin Tarayya>>Ministan Kwadago, Ngige

Ministan kwadago da samar da aiyuka, Chris Ngige, ya bayyana kwarin gwiwar cewa mambobin kungiyar Malaman Jami’o’i za su amince da sabon tayin da Gwamnatin Tarayya ta yi musu tare da kawo karshen yajin aikin na watanni takwas da ya fara a watan Maris.

 

Ya bukaci ASUU da ta hanzarta tuntubar mambobinta domin komawa kan teburin tattaunawa kafin ranar Juma’a.

Ngige yace “Ina jin cewa ko da wannan tayi na daya daga cikin mafi kyawu da suka samu tun lokacin da na fara sulhu da su. Ban ga dalilin da zai hana su karba ba. Duk abin da suka nema an basu. Ba na tsammanin ba zasu karbi wannan tayin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.