Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya baiwa gwamnatin tarayya shawarar ta baiwa ‘yan Bindiga kudin fansa dan su saki fasinjan jirgin kasa da suka kama a Kaduna.
Malamin yayi maganane a wajan wata addu’a ta musamman da jam’iyyar matan Arewa ta shirya kan kubutar da mutanen da aka yi garkuwa dasu.
Malamin yace ‘yan siyasa na ta fidda miliyoyin Naira suna sayen fom din takarar siyasa amma babu wanda yayi kokarin kubutar da mutanen da aka sace.
Malamin ya kara da cewa hakan bai dace ba.