Tsohon limamin masallacin Apo na ‘yan majalisun tarayya dake Abuja, Sheikh Nura Khalid ya bayyana cewa, cireshi daga mukaminsa ba komai bane.
Yace amma abinda yake baiwa gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari shawara shine ta nemi yafiyar ‘yan Najeriya saboda ta kasa cika musu Alkawuran data daukar musu.
Malamin yace bai yi nadamar kalaman da ya fada ba, maimakon haka ma dadi yaji saboda abinda suka masa sun kara daukakashine.