Majalisar wakilai ta bayyanawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa ya kamata ya dauko sojojin haya dan su taimakawa sojojin Najeriya magance matsalar tsaro.
‘Yan majalisar sun kuma yi kira ga shugaba Buhari da ya saka dokar ta baci akan harkar tsaro.
Majalisar ta bayyana hakane a zamanta na ranar Laraba.