fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Ya Kamata Musulmi Da Kirista Mu Kasance Masu Girmama Addinan Juna

Daga Mujanatu Diri

Ya kamata mu kasance masu girmama juna musamman a fannin addinin mu, kada musulmi ya ce zai wulakanta, tozarta ko cin zarafin Kiristia akan addinisa. Haka zalika kada kirista ya ce zai tozarta, cin zarafi da kuma wulakanta musulmi akan addininsa.

Yakamata ta kowane bangare mu sani cewa kamar yadda babban hadari ne ga musulmi ya je Kudu inda ya san kiristia suna da yawa ya ce zai ci zarafin su akan addinin su har yana tunanin zai kwashe lafiya. Haka zalika shi ma kiristia kada yayi tunanin zuwa Arewa ya ce zai ci zarafin addinin musulunci ya ce zai kwashe lafiya.

Karanta wannan  'Wasu 'Yan Nijeriya Sun Kama Kifi Mafi Sauri A Duniya Wanda Kudinsa Ya Haura Naira Dubu 600 Amma Sun Dafe Shi Sun Cinye

Addinin Musulunci bai koyar da mu mu ci zarafin kirista ko mu yi kalaman batanci ga Annabi Isah A.S (Yesu) ba.

Daga karshe ina kira da dukkanin shugabannin addinai da muke da su a Nijeriya da su ja hankalin membobinsu su kuma kara nuna musu illar cin zarafi da kuma tozarci ga Addini don gudun afkuwan baraka da kuma tashin hankali da rikicin addini.

Ina rokon Allah ya kara zaunar da kasa ta Nijeriya lafiya dama duniya baki daya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.