Tsohon Sanatan jihar Kaduna, Shehu Sani ya bukaci sauran ‘yan takarar shugaban kasa na zabe mai zuwa cewa su bayyan kadarorinsu kamar yadda dan takarar ACC yayi, wato Omoloye Sowore.
A ranar asabar 23 ga watan Yuli dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ACC Omoloye Sowore ya bayyana kadarorinsa, bayan kungiyar kare hakkin bil’adama ta SERAP ta bukaci hakan.
Inda yace motocinsa guda biyu ne Toyota Camry da kuma Lexus sai gidansa wanda bai wuce naira miliyan biyar ba, sai kuma yace yanada dala 300 a asusunsa kuma bayan wannan bashi komai sai taimakon ‘yan uwansa.
Sheu Sani ya jinjina masa kan bayyana kadarorinnasa daya yi, inda yace ya kamata sauran ‘yan takarar shugaban kasa dama sauran su duk suyi koyi dashi.