fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Ya kamata shugaba Buhari ya dawo da sojoji da ‘yansanda da suka yi ritaya a yaki ‘yan Bindiga dasu>>Afenifere ta bada shawara

Kungiyar kare muradun Yarbawa ta Afenifere ta baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari shawarar a dawo da tsaffin sojoji da ‘yansanda da suka yi ritaya dan su taya a yaki ‘yan Bindiga.

 

Kungiyar tace tunda sojojin yanzu sun kasa magance matsalar, ya kamata a kira tsaffin sojojin su taimaka.

 

Sakataren yada labaran kungiyar, Jare Ajayi ne ya bayyana haka.

 

Yace ya kamata shugaba Buhari ya cikawa ‘yan Najeriya Alkawuran da ya daukar musu na gyaran kasa.

 

Ya bayyana cewa, kasancewar shugaba Buhari ya nemi takarar shugabancin Najeriya sau 4 kamin yayi nasara, ya kamata ace ya fi kowane shugaba kawo ci gaba a kasarna .

Leave a Reply

Your email address will not be published.