fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Ya kamata shugaba Buhari ya saurari rokon Inyamurai kan sasantawa da kungiyar IPOB>>Sanata Shehu Sani

Sanata Shehu Sani ya baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari shawarar sasantawa da kungiyar IPOB.

 

Ya ce tunda dai su dattawan Inyamurai sun bada tabbacin cewa zasu tsayawa Nnamdi Kanu idan aka sakeshi, ya kamata shugaba Buhari ya sauraresu.

 

Sanata Sani dake neman takarar gwamnan jihar Kaduna ya bayyana hakane a shafinsa na Twitter inda yace babu abinda ba za’a iya yi ba dan samun zaman lafiya.

Dattawan Inyamurai dai a lokuta daban-daban sun sha rokon shugaba Buhari ya saki Nnamdi Kanu amma shugaban yana gaya musu cewa kotu ce ke da hurumin yanke masa hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published.