Itama tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta shiga sahun masu mayarwa da tauraron mawakin Hausa, Nazir Sarkin Waka Martani kan maganar Almajirci.
Nafisa Abdullahi ta fara maganar a daina haihuwar yaran da aka san ba za’a iya kul dasu ba ana jefarwa a titi.
Nazir Sarkin Waka ya mayar da martanin cewa, idan ana neman wanda iyayensu suka haifesu suka barsu ba tarbiyya, ba almajirai bane, a je Kannywood, watau masana’antar fina-finan Hausa.
Saidai Nafisa ta mayar da martani inda tace Nazir dan neman sunane, sannan ta kalubalanceshi da ya fito ya fadi sunan da wa yake.
Lamarin ya jawo cece-kuce sosai tsakanin mutane musaman masu bibiyar harkar fina-finan Hausa da masu kare muradun Almajici.
Taurarin fina-finan Hausa da yawa sun mayar wa da Nazir Sarkin Waka da martani, ciki Hadda Rahama Sadau wadda itama ta shiga sahu.
Rahama a nata martanin tace “Irin Maganganu Haka Basa Birgeni, Mutum Ya fito ya Fadi Sunan Wanda yakeyi dashi tunda yace ba da Wanda ake Zargi yakeyi ba. 🤔 Hau’shin Banza Da Wofi Kawai! Mtswwwww!!! 😤”