Abdullahi Mohammed, dan gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su guji yunƙurin sanya dukkan mambobin ƙabilun a matsayin masu satar mutane, karuwanci, dillalan kwayoyi da kuma masu damfara ta yanar gizo.
Abdullahi ya yi wannan kiran ne a yau biyo bayan sace-sacen mutane da kashe-kashe a wasu sassan kasar da ake zargin Fulani makiyaya da aikatawa.
Ya daura wani hoto wanda ya nuna kabilu daban-daban a Najeriya da kuma laifukan da mutane suka alakanta su.