Ana zargin wannan matashin da kashe wani da ya je rabasu fada a jihar Bauchi.
An kama matashin, Idriss Baba Saje me shekaru 32 ne a karamar hukumar Dass dake jihar bayan ya kashe Yunusa Garba ta hanyar daba masa wuka.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil ya bayyana cewa, Idris ya dabawa Garba wuka a kirji ne bayan da Garban ya je rabasu fada shi da wani manajan Otal.
Garba dan shekaru 25 da ya fito daga yankin Gwallaga na jihar Bauchi.
Ana ci gaba da bincike kan lamarin.