INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN
Ya Rasu Bayan Makonni Biyu Da Ɗaura Masa Aure.
Daga Hon. Saleh Shehu Hadejia
Ya rasu sakamakon haɗarin mota da ya rutsa da shi daga garin Kano zuwa Haɗejia a Jihar Jigawa.
Matashin mai suna Hamza Muhammad Mai Wando, satin sa biyu yau da ɗaura aurensa, sannan ma’aikaci ne a Gidan rediyon Sawaba dake cikin garin Haɗejia.
Za a yi jana’izarsa a gobe Juma’a a garin Dingare dake ƙaramar hukumar Kaugama a Jihar Jigawa.