Tsohon ahugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya mika sakon ta’aziyyar sa ga gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun kan mutuwar Sanata Buruji Kashamu.
Sanata Ben Bruce ne ya sanar da mutuwar Buruji Kashamu wanda Coronavirus/COVID-19 ta kashe.
Obasanji ta bakin me magana da yawunsa, Kehinde Akinyemi yace mutuwar Kashamu abin bakin ciki ce amma kuma darasi ce ga mu da muke doron kasa.
Yace Lokacin Kashamu na raye yayi amfani da Siyasa da kwarewa wajan kaucewa Shari’ar laifukan da ake masa a Najeriya da kuma kasashen waje.
Yace amma idan fa lokacin Mutuwa yayi babu wanda ya isa ya hana mahaliccin mu daukar ranmu. Yace yana fatan Allah ya gafarta masa ya kuma sakashi Aljannah sannan ya baiwa iyalansa juriyar rashi.
Kamin mutuwarsa, Kashamu ya sha fama da shari’a kan safarar miyagun kwayoyi.