Daga Abdurrahman Sada Shinkafi
‘Yan bindiga sun ƙaddamar da mummunan hari a garin Shinkafi, bayan katsewar layikan sadarwa a ƙaramar hukumar.
Ƴan bindigar sun cigaba da ƙoƙarin afkawa garin na Shinkafi, wanda sun shigo garin shekaran jiya sun kashe mutum biyu sun jikkata wasu.
Haka zalika sun shigo a larabar nan, sun kashe mutum uku sun raunata wasu.
Wannan shi ne dalilin da ya sa mu ke zargin gwamnati a wannan sha’ani, kasancewar babu wani matakin gaugawa da gwamnati ke ɗauka bayan jin abinda ke faruwa.
Kuma akwai alamar tambaya cikin ɗauke network a ƙaramar hukumar.
Ta hanyar yadda aka yanke layikan a siyasance.
Da farko an fara yanke layin Airtel, bayan wasu kwanaki aka yanke Etisalat, bayan wasu kwanaki aka yanke MTN, ƙarshe aka yanke GLO.
Allah mun kawo ƙara a wurin ka, ka saka ma na wannan zalunci da ake yi mu na.