Gwajin ciki da fitsari shine mafi bada sakamako me kyau.
Idan dai an yi gwajin bayan kwanaki 10 zuwa 14 da yin jima’i to lallai za’a ga sakamako me kyau sosai.
Akwai hanyoyi da yawa da ake amfani dasu wajan gwajin ciki da fitsari amma wanda suka fi shahara kuma likitoci suka fi yadda dashi shine na tsinken gwajin ciki da ake sayarwa a kyamis.
Ana samun mazubi ne ko kofi sai a yi fitsarin a ciki si a saka Rabin tsinken gwajin cikin a ciki, sai ki yi kamar kina kirge da yatsunki, ki kirga 7 ko 10, shikenan sai a cire, a ajiye shi a kwance.
Yawanci za’a iya ganin sakamakon gwajin cikin minti 1 ko zuwa 5.
Idan tsinken ya nuna layi biyu to kina da ciki amma idan ya nuna layi daya, baki da ciki.
Masana sunce zai fi kyau a bari sai an yi batan wata kamin a yi duk wani gwajin daukar ciki ko kuma bayan kwaki 14.