Thursday, July 18
Shadow

Yadda ake saduwa da amarya daren farko

Da farko dai tunda har ake wannan tambaya, an daura aure ko ana daf da daurawa, dan haka muna tayaku murna.

Bayan Abokai da kawaye sun tafi, zai kasance sauran kai kadai da amaryarka.

Zaku yi Sallah raka’a biyu ku godewa Allah bisa wannan ni’ima da ya muku na zama mata da miji.

Sannan zakawa matarka addu’a kamar haka:

ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻰ ﺃَﺳْﺄَﻟُﻚَ ﺧَﻴْﺮَﻫَﺎ ﻭَﺧَﻴْﺮَ ﻣَﺎ ﺟَﺒَﻠْﺘَﻬَﺎ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﻚَ ﻣِﻦْ ﺷَﺮِّﻫَﺎ ﻭَﻣِﻦْ ﺷَﺮِّ ﻣَﺎ ﺟَﺒَﻠْﺘَﻬَﺎ ﻋَﻠَﻴْﻪ

” ALLAHUMMA INNEE AS’ALUKA KHAIRAHA WA KHAIRA MA JABALTAHA ALAYYA WA A’UZUBIKA MIN SHARRIHA WA SHARRI MA JABALTAHA ALAIYAYA 

Fassara:  “Ya Allah ina roqonKa alherinta da alherin da ka hallice ta a kansa, kuma ina neman tsari daga sharrinta da sharrin da Ka hallice ta a kansa.  (Abu Dawud da Ibn Majah da Ibn Sinni suka rawaito).

Karanta Wannan  Addu'a ga mijina

Daga nan, zaku ci kazarku ko tsire da abin shan daka kawo.

Bayan nan sai a wanke hannuwa da baki.

Ka umarci amaryarka ta cire kaya.

Ku hau gado. Idan akwai gajiya a tare daku, ba lallai sai kun yi saduwar aure a wannan dare ba.

Amma idan babu gajiya a tare daku, sai a dauki harama, ka taimakawa matarka ta cire kayan dake jikinta.

Ta zama daga ita sai rigar mama da dan kamfai ko kuma irin yanda kake bukata, idan ma gaba dayan kayan kake so ta cire, to dai ta zama taka.

A dan taba wasanni da hira irin ta masoya, da wasa da juna da sumbata.

Karanta Wannan  Kwana nawa mace take daukar ciki

Kamin ka kai ga fara jima’i da matarka.

Ya kamata ka karanta wannan addu’a.

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺟﻨﺒﻨﺎ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ، ﻭﺟﻨﺐ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻣﺎ ﺭﺯﻗﺘﻨﺎ

“Allahumma jannibnash shaitan wajannibish -shaytana ma razaktana”

FASSARA:  “Ya Allah Ka nesantar da ni daga shaidan kuma Ka nesantar da shaidan daga abin da Ka azurtamu da shi (Na ’ya’ya), (Bukhari da Muslim ne suka fitar da shi daga Abbas).

ANNABI ( S.A.W) yace “idan aka kaddara samun ciki a wannan saduwar to shaidan ba zai iya cutar dashi ba har abada.

Hakazalika, bayan an kammala ibadar aure ma akwai addu’ar da ake gabatarwa. Ga addu’ar:

“Allahumma lataj’al shaidana fiyma razaqtani nasiban.”

Karanta Wannan  HOTUNAN BIKI: Hajiya Dakta Maryam Shetti ta yi aure

FASSARA:   “Ya Allah Kada Ka sanya shaidani ya zamo yana da rabo cikin abin da Ka azurtamu.(Bukhari da Muslim).

Bayan kammala jima’i, an so a yi wanka, amma idan wanka be samu ba, sai a yi alwala.

Daga nan, ka ganta tsirara itama haka.

Dan haka kada wannan yasa ku daina ganin girman juna.

Ya kamata ku ci gaba da girmama juna da mutunta juna, da yin abubuwan da zai kara muku son juna da tausayawa juna.

Yana da kyau ku rika fadawa juna kalaman yabo da soyayya, kuma yana da kyau kowanne daga cikinku ya rika tsaftace kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *