Tankar danyen mai ta kama da wuta ta babbake a kusa da gadar Warewa dake babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a jihar Ogun.
Hukunar dake bayar da agajin gaggawa ta FRSC ce ta bayyana hakan inda tace motoci uku da mazaje uku ne wannan iftila’in ya faru dasu.
Hukumar ta kara da cewa cikin mutane ukun daya kadai ya samu rauni kuma an kai shi asibiti sannan babu wanda ya mutu a cikin su.