fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Yadda Barcelona ta sayar da kadarorinta ta sayo sabbin ‘yan wasa a wannan kakar

Kungiyar Barcelona ta gina tawagarta sosai a wannan kakar domin ta lashe kofuna kuma ta faranta ran masoyanta a kakar bana.

Inda ta sayo manyan ‘yan wasa kamar su Robert Lewndowski, Frank Kessie, Joules Kounde da Andreas Christensen da kuma Rafinha.

Barcelona ta sayar da wasu kadarorinta da dama kamar ta fannin talabijin dinta da dai sauransu, wanda kudin suka kai har yuro miliyan shida.

Kuma Barca har yanzu dai bata yiwa sabbin ‘yan wasan nata rigista ba amma tana so tayi amfani da wa’yan nan kuden tayi masu rigistar kafin a fara buga wannan kakar a karshen mako.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.