fbpx
Saturday, June 25
Shadow

Yadda gwamnatin Lagos ta jefa ‘yan kasuwar dabbobi ta Alaba Rago cikin zulumi

‘Yan kasuwa a babbar kasuwar dabbobi ta Alaba Rago da ke birnin Lagos na Kudancin Najeriya sun shiga zulumi bayan da gwamnatin Jihar ta ba su wa’adin kwanaki 14 su fice daga cikinta.

Gwamnatin Jihar ta ce za ta dauki matakin ne domin samun damar inganta kasuwar da fasali irin na zamani.

Rundunar ‘yan-sandan Jihar ta bayyana cewa sanarwar korar ‘yan kasuwar daga Alaba Rago ta fito ne bayan tattaunawar da gwamnatin Jihar ta yi da wakilan ‘yan kasuwar.

Ta kara da cewa ana samun matsalolin rashin tsaro da ke faruwa a kasuwar da ma yankin.

Sai dai ‘yan kasuwar sun bayyana kaduwarsu da samun labarin sauya musu matsuguni ba tare da yin shiri ba bayan sun shafe kimanin shekara hamsin suna kasuwanci a wurin.

Shugaban kasuwar, Sarki Umaru Nagoggo, ya shaida wa BBC cewa sanarwar ta zo musu da mamaki.

A ‘yan makonnin da suka gabata jami’an tsaro sun kama wasu matasa dauke da bindigogi a yankin na kasuwar Alaba Rago- kuma hukumomi sun yi zargin cewa sun fito daga kasuwar ce kuma suna samun mafaka a can.

Alhaji Adamu Katagum, Wazirin kasuwar Alaba Rago ya shaida wa BBC cewa wannan sanarwa ta jefa su cikin zulumi ganin cewa suna kasuwanci da makwabtan kasashe kamar Jamhuriyyar Benin da Togo da Ghana da sauransu.

Ya kara da cewa a shirye suke su inganta kasuwar da tsari daidai da bukatar gwamnatin Jihar Lagos, amma batun su tashi ba ta taso ba.

Bayanai sun nuna cewa shugabannin al’ummar arewacin Najeriya, karkashin marigayi Sarkin Hausawan jihar Legas, Alhaji Yaro Dogara, ne suka nemi izinin gina Kasuwar Alaba, kusan shekara hamsin da suka gabata, wadda ta amince.

Rahotanni sun ce fiye da kashi saba’in daga mazauna kasuwar dai sun fito daga arewacin Najeriya ne.

Ko a jiya an yi mummunan rikici tsakanin ‘yan okada da ‘yan sanda a kan babban titin Legas zuwa Badagry – hanyar da ke kai wa ga babbar kasuwar ta Alaba Rago.

Hakan ya sanya ake gargadin mutane da su yi hattara kan abubuwan da ke kai wa suna komowa sakamakon rikici da yanzu ake zaman dardar tsakanin ‘yan sanda da masu baburan haya kan hanyar Lagos zuwa Badagry.

Gwamnatin Jihar Lagos dai na zargin cewa shugabannin kasuwar ba sa daukar matakan kula da tsaronta suna masu cewa ta zama matsugunin bata-gari, ko da yake shugabannin sun sha musanta zargin.

Yanzu haka shugabannin na wani zama tare da shirin aike wa da wasiku ga daukacin gwamnonin da sarakuna da sauran masu fada a ji daga arewacin kasar don su bai wa gwamna Babajide Sanwo-Olu baki da kar a tashe su daga kasuwar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.